Jamus

Ambaliyar ruwa: Jamus ta nemi karin mutane 15,000 da su fice daga gidajensu

Wani yanki da amblaiyar ruwa ya mamaye a Nahiyar Turai
Wani yanki da amblaiyar ruwa ya mamaye a Nahiyar Turai

Hukumomin Kasar Jamus sun bukaci karin mutane 15,000 da su bar gidajen su, saboda barazanar ambaliyar ruwa daga kogin Elbe, wanda ke kara barazana ga kasar Hungary.

Talla

Ambaliyan ya sanya dubban mutane sun shiga aikin agaji dan taimakawa wadanda bala’in ya shafa, da kuma ganin kwashe wadanda basu bar gidajen su ba.

Mafi aksarin wadanda suka fice daga gidajensu tun farko na zaune ne tare da ‘yan uwa da abokan arziki kamar yadda rahotanni ke nunawa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI