Syria

Dakarun Syria sun mayar da hankali wajen kwato garin Aleppo

Wani yankin Aleppo
Wani yankin Aleppo REUTERS/Muzaffar Salman

Kwanaki kadan bayan dakarun Syria sun kwace garin Qusayr daga hannun ‘yan tawaye, bayanai na nuna cewa yanzu haka suna shirin kutsa kai zuwa karbo garin Aleppo daga ‘yan tawaye.

Talla

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa bayan nasarar da dakarun Syrian suka yi na kwace wannan gari na Qusayr dake kan iyakan Lebanon da taimakon mayakan Hizbullah, yanzu dakarun sun doshi sake kwace yankin garin Aleppo dake hannun ‘yan tawaye.

Majiyoyi na cewa Dakarun Gwamnati dubbai na chan suna haraman kutsa kai yankin.

Tun a jiya Lahadi bayanai ke cewa wasu mutane a yankin Qusayr ke ta karade yankin suna murna da daga hotunan shugaba Bashar al-Assad bayan nasarar da dakarun kasar suka samu.

Wasu bayanan daga Beirut da Lebanon na cewa an harbi wani mutun a wuya, a wajen Ofishin jakadancin kasar Iran yayin wani bore saboda zargin hannun da kungiyar Hizbullah ke dashi a rikicin Syria.

Masu aikin agaji a Lebanon sun bayyana cewa akwai mutane da yawa da aka jikkata kuma aka tsallaka dasu domin ayi masu magani.

A cewar Sakataren Waje na Britaniya, William Hague nasarar da dakarun na Syria suka samu zai haifar da tarnaki wajen taron sulhu da kasar Amurka da Rasha suka tsara, don warware rikicin Syrian daya kwashe watanni 26

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI