Yemen
Jami’an tsaro sun hallaka ‘Yan tawaye 10 a Yemen
Wallafawa ranar:
Jami’an Tsaro a kasar Yemen, sun hallaka ‘yan tawayen kasar mabiya Shi’a 10, yayin da suka raunata wasu 38 a fafatawar da suka yi a gaban ofishin jami’an dake Sanaa.
Talla
Rahotanni sun ce an samu arangamar ne sakamakon mamaye ofishin jami’an tsaron, dan neman ganin an sake ‘yan uwan ‘yan Shi’an da aka tsare, inda suka kai hari da bindiga da kuma gurneti.
Rikici tsakanin ‘yan Shi’an da jami’an tsaron kasar ta Yemen ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu