Africa ta Kudu

Kwararrun likitoci sun dukufa wajen shawo kan rashin lafiyar Mandela

Tsohon shugaban kasar Africa ta Kudu, Nelson Mandela
Tsohon shugaban kasar Africa ta Kudu, Nelson Mandela REUTERS/Jonathan Evans/File

‘Yan kasar Afrika ta Kudu na ci gaba da gudanar da addu’o’in fatan samun sauki ga tsohon shugaban kasar, Nelson Mandela a yayin da ya shiga rana ta uku yana jinya a asibiti. Da sanyin safiyar Juma’a ne dai aka garzaya da Nelson Mandela zuwa asibiti bayan ciwon matsanancin sanyi na Pneumonia da yake fama da shi ya tashi.  

Talla

Wannan dai shine karo na hudu cikin watanni bakwai da ake kwantar da Mandela a asibiti a yayin da yake daf da cika shekaru 95 a wata mai zuwa.

Rahotanni na nuna cewa halin da lafiyarsa ta shiga ya tsananta sai dai bai fita daga cikin hayyacinsa ba, wanda hakan yasa ake ta gudanar da addu’o’i a mujami’u, domin neman mai sauki, yayin da Jam’iyarsa mai mulki ta ANC a kasar ta mika nata sakon fatan samun sauki ga tsohon shugaban.

Tuni itama Fadar White House ta hanun Kakakin Kwamitin tsaron kasar, ta mika sakon fatar samun sauki ga tsohon shugaban kasar na Afrika ta Kudu.

Shugaban kasar Jacob Zuma dai ya bayyanawa manema labarai cewa Mandela, yana samun kyakyawan kula daga kwararrun likitoci wadanda ke iya bakin kokarinsu na suga cewa ya samu lafiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.