UNESCO-Najeriya

Matsalar karatun yara kanana ta fi kamari a Najeriya-UNESCO

Yara suna koyon hura mabusar Pawpaw a kasar Uganda
Yara suna koyon hura mabusar Pawpaw a kasar Uganda UNESCO

Hukumar kula da ci gaban Ilimi da kimiya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO), ta ce Najeriya ce kasar da aka fi samun yawan yaran da ba su zuwa makaranta fiye da sauran kasashen duniya. Rahoton hukumar yace yara kanana sama da Miliyan Hamsin ne a duniya ke zaman banza.

Talla

Amma kuma an yi hasashen za’a iya samun ci gaba a bangaren makarantar Firamare kafin 2015.

Duk shekara hukumar takan fitar da irin wannan rahoton wanda ke auna mizanin ci gaban da aka samu a duniya ta bangaren ilimin yara kanana.

A shekarar 2010 hukumar tace kimanin yara kanana Milyan 61 ne ba su zuwa makaranta.

A rahoton na bana, an bayyana samun raguwar wadanda ke tallafawa ilimi a duniya da kashi 6 wanda hakan ke nuna Birtaniya ita ce a sahun gaba da ke tallafawa hukumar UNESCO. Wannan kuma ya biyo bayan datse kasafin kudin Amurka.

Rahoton yace an samu karuwar tallafi daga kasashen Jamus da Australia da Norway, amma Faransa da Japan da Holland da Canada dukkaninsu sun datse kasafin kudin da suke tallafawa hukumar.

Rahoton hukumar yace matsalar rashin ilimin yara kanana ta fi kamari a kasashen Afrika da ke kudu da Sahara, kuma Najeriya ce a sahun gaba.

A watan Mayu, Mista Jean Gouch wakilin hukumar UNICEF a Najeriya yace kimanin yara kanana Miliyan 10.5 ne ba sa zuwa makaranta, yana mai cewa matsalar ta yi kamari ne saboda matsalar tsaro da ke addabar yankin arewacin kasar.

A yankin kudanci da yammacin kasashen Asiya, rahoton UNESCO yace an samu ci gaba da kashi daya cikin uku na yaran da ba su zuwa makaranta.

Kodayake, rahoton UNESCO yace an samu ci gaba a kasashen Habasha da Uganda a Nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.