Wasan Tennis

Nadal ya lashe kofin Roland Garros karo na takwas

Rafael Nadal bayan ya lashe gasar Roland Garros
Rafael Nadal bayan ya lashe gasar Roland Garros REUTERS/Vincent Kessler

Dan wasan Tennis na uku a duniya, Rafael Nadal ya lashe kofin gasar Roland Garros bayan doke David Ferrer da ya yi da ci 6-3, 6-2,6-3 a wasan karshen da aka buga a jiya. Wannan nasara day a samu ta sa ya kafa tarihi a matsayin dan wasan Tennis na farko a duniya da ya lashe gasar sau takwas.  

Talla

Dan shekaru 27, Nadal ya fashe da kuka a yayin da ake daga tutar kasarsa ta Spain daf da za a mika mai kofin da ya lashe.

A yanzu haka ya lashe kofunan gasa daban daban guda bakwai ke nan tun bayan dawowarsa daga jinya da ya yi na watanni bakwai, wacce ta sa ya kasa halartar gasar Olympic da gasar Australian Open da kuma ta US Open.

David Ferrer wanda wannan shine karo na farko da ya taba halartar wasan karshen wannan gasa ya ce Nadal ya cancanci ya lashe kofion gasar domin kwarwarsa.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI