Kwallon kafa

Sakamakon wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya a yankin Nahiyar Afrika

Taswirar nahiyar Afrika
Taswirar nahiyar Afrika www.vbmap.org

Sakamakon wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da aka buga a karshen mako na nuna cewa a rukunin A, Botswana ta sha kayi a hanun Habasha da ci 2-1, Afrika ta Kudu ta doke Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da ci 3-0.

Talla

Habasha ce dai ke saman teburin wannan rukuni da maki 10, Afrika ta kudu na jeri na biyu da maki 8.

A rukunin B kuwa, Tunisia da Sierra Leone sun ta shi da ci 2-2 yayin da Cape Verde Island ta doke Equatorial Guinea da ci 2-1.

Tunisia ce dai ke jagorantar teburin da maki 10 kana Sierra Leone na jeri na biyu da maki 5.

A rukunin C kuwa Gambia ta sha kayi a hanun Cote D’Ivoir da ci 3-0 a yayin da Morocco ta lallasa Tanzania da ci 2-1.

Cote d’Ivoir ce dai a saman teburin rukunin da maki 10, Tanzania kuma na jeri na biyu da maki 6.

Har ila yau a rukunin E kuwa a birnin Niamey Nijar ta sha kayi a hanun Burkina Faso da ci 1-0, Gabon da Congo Brazzaville sun ta shi canjaras.

Congo ce dai ke jagorantar teburin wannan rukuni da maki 10, kana Burkina Faso na jeri na biyu da maki 6.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI