Mali

An shiga rana ta uku a tattaunawar gwamnatin Mali da ‘Yan tawaye

Shugaban kasar Burkina Faso, Blaise Compare a lokacin ganawa da 'yan tawaye a Ouagadougou
Shugaban kasar Burkina Faso, Blaise Compare a lokacin ganawa da 'yan tawaye a Ouagadougou AHMED OUOBA / AFP

An shiga rana ta uku a ci gaba da gudanar da tattaunawar samar da zaman lafiya da ake yi a birnin Ouagadougou dake Burkina Faso, tsakanin wakilan gwamnatin Mali da na kungiyar ‘yan tawayen MNLA da ke mamaye da yankin Kidal na Arewacin kasar.

Talla

Tattaunawar wadda aka soma a ranar Asabar da ta gabata karkashin jagorancin shugaban kasar Burkina Faso mai shiga tsakanin na kungiyar ci gaban tattalin arzikin yankin yammacin Afrika Blaise Compaore, na matsayin wani zakaran gwajin dafi dangane da makomar Mali da ke shirin gudanar da zaben shugaban kasa a cikin watan Yuli mai zuwa.

Babban mai shiga tsakanin Blaise Compaare, ya ce dakatar da fada ita ce hanya mafi a’ala domin gudanar da wannan zabe a cikin tsanaki, kuma ta hakan ne kawai gwamnatin Mali za ta iya wanzar da mulkinta har ma da aikewa da jami’anta zuwa sauran sassa na kasar da har yanzu ke a karkashin ikon ‘yan tawaye.

To sai dai wani abu da ake kallo a matsayin karfen kafa da zai iya hanawa tattaunawar kankama kamar yadda ake bukata shi ne yadda ‘ya tawayen MNLA ke cewa ba za a iya yin tattaunawar ba a daidai lokacin da rahotanni ke cewa dakarun gwamnati na shirin kai hari domin kwato garin Kidal daga hannunsu, suna cewa yin hakan abu ne da zai iya gurgunta tattaunawar.

Ko baya ga kungiyar ta MNLA da ke halartar wannan tattaunawa ta birnin Ouagadougou, rahotanni sun ce akwai wakilan wata kungiyar Azbinawa mai suna HCUA da ke neman ita ma a ba ta damar jin ta bakinta a game da shirin samar da zaman lafiya a kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI