FIFA-Najeriya

Najeriya na dab da tsallakewa zuwa gasar cin Kofin Duniya a Brazil

Stephen Keshi Kocin Super Eagle na Najeriya
Stephen Keshi Kocin Super Eagle na Najeriya EUTERS/Siphiwe Sibeko

Kasar Malawi ta bude wa Najeriya kofar tsallakewa zuwa gasar cin kofin Duniya a Brazil bayan sun tashi wasa ci 2-2 da Kenya. Tazarar maki daya ne yanzu Najeriya ta ba Malawi a rukuninsu na F, amma tazarar za ta koma maki hudu idan har ‘Yan wasan Super Eagles suka samu nasarar doke Namibia idan an jima.

Talla

Idan dai Najeriya ta samu nasara za ta kasance kasa ta farko daga Afrika da ta tsallake zuwa gasar cin kofin duniya da za’a gudanar a badi a kasar Brazil.

Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da Najeriya ke shirye shiryen shiga gasar cin kofin zakarun Nahiyoyin Duniya da za'a fara karawa a karshen makon a Brazil.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.