Najeriya

Ado Bayero ya cika shekaru 50 a Masarautar Kano

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan tare da Mai Martaba Ado Bayero, Sarkin Kano
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan tare da Mai Martaba Ado Bayero, Sarkin Kano REUTERS/Stringer

An Kammala bukukuwan cika shekaru 50 da hawa karagar mulkin Sarkin Kano, Dr Ado Bayero, inda aka gudanar da addu’oi da kuma hawan Durba, wadda ta samu halartar dubban mutane daga kowanne sako na duniya. Cikin wadanda suka halarci bikin sun hada da mataimakin shugaban Najeriya, Namadi Sambo da Janar Muhammadu Buhari da Janar Abdulsalami Abubakar, da Mai Martaba Sarkin Musulmin Najeriya da Sarakuna daga ciki da wajen kasar. Wakilinmu Abubakar Issa Dandago

Talla

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.