Korea ta Arewa

Amurka ta yi maraba da tayin Korea ta Arewa amma...

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama

Kasar Amurka ta yi maraba da tayin tattaunawar da Korea ta Arewa ta yi mata, sai dai ta ce hakan ba zai hana kasar kaucewa daga bukatun dake gaban ta na Majalisar Dinkin Duniya ba, na ganin ta dakatar da shirin ta na mallakar makamin nukiliya.

Talla

Babban hafsa a fadar shugaban Amurka, Denis McDonough, ya ce dama matsayin Amurkan shine warware matsalar kasar ta hanyar tattaunawa, sai dai ya kara da cewar, dole ne tattaunawar ta zama na gaskiya da kuma mutunta kudirorin dake gaban su.

A dai karshen makon da ya gabata kasar Korea ta Arewan, ta nuna shirinta na tattaunawa da kasar ta Amurka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI