Turkiya

Manyan Kungiyoyin kwadago a Turkiya sun yi kiran yajin aikin gama-gari a yau

Ana zargin 'Yan sanda da amfani da karfin tuwo wajen tarwatsa masu zanga zanga a Turkiya
Ana zargin 'Yan sanda da amfani da karfin tuwo wajen tarwatsa masu zanga zanga a Turkiya

Biyu daga cikin manyan kungiyoyin kwadagon kasar Turkiya, sun yi kiran yajin aikin gama gari a yau, saboda abinda suka kira yadda 'yan Sanda ke amfani da karfin da ya wuce kima kan masu zanga zanga.

Talla

Kakakin kungiyar kwadagon KESK, Baki Cinar, ya ce daukacin 'ya'yan kungiyar dake Turkiya ne za su shiga yajin aikin, tare da wasu takwarorinsu.

A bangare daya, Firaministan kasar, Recep Tayyip Erdogan, ya kare matakin da ya dauka a kan masu zanga zangar, inda ya ke cewa hakkin sa ne ya kawo karshen tashin hankalin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI