Syria

Putin da Cameron na ci gaba da samun sabanin ra’ayi kan shawo rikicin Syria

Firaministan Birataniya, David Cameron (Dama) da Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin (Hagu) a lokacin da suke ganawa da manema labarai bayan wata tattaunawa da suka yi
Firaministan Birataniya, David Cameron (Dama) da Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin (Hagu) a lokacin da suke ganawa da manema labarai bayan wata tattaunawa da suka yi

Banbancin ra’ayi tsakanin Shugaba Vladimir Putin na Rasha da Firaministan Birtaniya, David Cameron na kara bayyana game da rikicin Syria a yayin da Putin ya kare matsayinsa na aikewa da makamai zuwa ga gwamnatin kasar Bashar al Assad. 

Talla

Jim kadan bayan wata tattaunawa da su ka yi da Firaministan Birtaniya, David Cameron, Shugaban Rasha, Vladimir Putin a lokacin ganawa da manema labarai, ya yi kira ga sauren kasashe takwas masu karfin tattalin arziki a duniya da su bi ka’idojin da aka shimfida idan har za su aika da makamai zuwa kasar ta Syria.

Putin ya ce bai dace a aikawa da 'yan tawaye makamai ba saboda irin salon da suka dauka a yakin wanda ya nuna hotan bidiyon wani mutum ya na cin hantar wani sojan Syria da suka kashe.

Sai dai Firaministan na kasar Birtaniya, David Cameron ya ce sam bai yadda da matsayar da Putin ya dauka ba domin shugaba Bashar al Assad shike da alhakin rayukan dake salwanta a kasar ya kuma nuna muhimmancin kaiwa ‘yan tawayen kasar dauki.

A dai yau ne aka bude taron na kasashen G8 a Arewacin Ireland wanda Cameron zai jagoranta, kuma baya ga wasu batutuwa da za a tattauna, batun na Syria na daya daga cikin batutuwan da ake sa ran zai mamaye taron.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI