Syria-G8-Korea

Rikicin Syria zai mamaye taron kasashen G8

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama a lokacin da ya isa taron kasashen G8 a Arewacin Ireland
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama a lokacin da ya isa taron kasashen G8 a Arewacin Ireland REUTERS/Kevin Lamarque

Kokarin sasanta rikicin Syria da matsalar biyan haraji da matakan tsuke bakin aljihu su ne muhimman batutuwan da za su mamaye taron kasashen G8 masu karfin tattalin arzakin duniya na kwanaki biyu da Birtaniya ke jagoranta.

Talla

Taron kasashen na G8 na zuwa ne a dai dai lokacin da mutane musamman daga Turai ke boren neman manyan kasashen sun tunkari matsalar talauci a duniya.

Batun inganta tsarin haraji da inganta huldar kasuwanci su ne dai muhimman batutuwan da Birtaniya za ta jagoranta a taron manyan kasashen da suka hada da Amurka da Japan da Jamus da Faransa da Canada da kuma Rasha.

Kaucewa biyan haraji dai matsala ce da ake fuskanta daga attajiran Turai musamman badakalar da ta shafi Ministan kasafin kudin Faransa. Lamarin da gabanin taron, Shugaban Faransa, Francois Hollande ya ce za su yi yaki da matsalar a Turai da ma duniya baki daya.

A dai dai lokacin da kasashen ke fuskantar bore game da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati, ana sa ran za su dauki mataki akan kamfanoni irinsu Google da Amazon da Apple wadanda ake zargi suna biyan harajin da be taka kara ya karya ba a kasashen da suke cin kasuwa.

Wani batu kuma da zai mamaye taron na G8 shi ne batun kawo karshen rikicin Syria, da kuma rikicin nukiliyar Iran duk cewa nan ba da jimawa za’a samu sauyin gwamnati a kasar ta Iran.

A wata waskika zuwa ga gwamnatin Birtaniya,  Paparoma Francis ya yi kira ga kasashen na G8 da su gaggauta daukar matakan kawo karshen rikicin na Syria, yana mai kira ga sauran kasashen su lallashi Rasha domin daukar matakin da ya dace domin kawo karshen rikicin da ya lakume rayukan mutane kusan 100,000.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI