Rose ya lashe gasar US Open a wasan Lambu
Wallafawa ranar:
Justine Rose ya lashe gasar US Open a fagen wasan kwallon lambu, wanda hakan ya bashi damar danewa matsayi na uku a zakarun ‘yan wasan kwallon ta lambu.
Talla
Wannan nasara da Rose, dan shekaru 32 ya samu ta kuma bashi damar zama dan kasar Birtaniya na farko da ya lashe gasar ta US Open tun bayan shekarar 1970.
Har yanzu dai Tiger Woods shine a matsayi na farko a zakarun duniya a yayin da McIlroy ke ci gaba da kasancewa a matsayi na biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu