Kwallon kafa

Sakamakon wasannin cin kofin zakarun nahiyoyin duniya

'Yan wasan Italiya
'Yan wasan Italiya

A cigaba da karawar da ake yi a fagen gasar cin kofin zakarun nahiyoyin duniya, a jiya kasar Italiya ta doke kasar Mexico da ci 2-1, inda Mario Balotelli ya zirawa italiya kwallo ta biyu a cikin minti na 78, wacce ta banbanta bagarorin biyu bayan sun yi kunnen doki da farko. 

Talla

Ita kuwa mai masaukin baki, Brazil ta doke Japan ne da ci 3-0, kana zakarun duniya, wato Spain suma sun fara wasansu ne da kafar dama, inda suka lallasa Uruguay da ci 2-1.

A yanzu haka Brazil ce ke saman teburin rukunin A da maki uku, inda take biye da Italiya da maki uku a yayin da a rukunin B kuwa Spain ke sama da maki uku.

a Yau kuma Najeriya za ta fafata da kasar Tahiti a wasannin bangarorin biyu na farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI