Syria

Syria ta zargi Masar da yunkurin haifar da rarrabuwan kawuna a Gabas Ta Tsakiya

Shugaban kasar Syria, Bashar al- Assad
Shugaban kasar Syria, Bashar al- Assad

Kasar Syria ta zargi Masar da yunkuri haifar da rarrabuwar kawuna a Yankin Gabas ta Tsakiya, sakamakon matakin da kasar ta dauka na soke duk wata huldar Jakadanci da kasar.

Talla

Ministan harkokin wajen Ayria ne ya sanar da haka, a dai dai lokacin da aka ruwaito kasar Saudi Arabia na shirin baiwa ‘Yan tawayen Syrian garkuwan kakkabo rokoki da jiragen sama.

Rikicin na Syria wanda aka kwashe shekaru fiye da biyu ana yi, ya yi asarar rayukan mutane kusan 100,000 a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.