Nijeriya

Yan bindiga sun hallaka mutane kusan 50 a Jihar Zamfara dake Nijeriya

Kizara, dake karamar hukumar Tsafe.
Kizara, dake karamar hukumar Tsafe. REUTERS/Stringer

A jihar Zamfara dake Nijeriya wasu Yan bindiga sun hallaka mutane kusan 50 a Kizara, dake karamar hukumar Tsafe.Yan fashin sun je kauyen ne da asubahin ranar talata , inda suka abkawa mutanen garin, inda suka kashe mutane da dama, cikinsu harda limamin garin da wani Basarake.Jihar Zamfara na daga cikin Jiihohin dake fama da matsalar rashin tsaro gani yadda yan bindiga ke ciggaba da tayar da hankulan jama’a, abinda yake jefa shakku kan rawar da jami’an tsaro ke takawa a jihar.