Brazil

Komi na iya faruwa a wasan Najeriya da Spain, inji Keshi

Fernando Torres yana tabewa da Raúl Albiol a Filin wasa na Maracana da ke birnin Río de Janeiro.
Fernando Torres yana tabewa da Raúl Albiol a Filin wasa na Maracana da ke birnin Río de Janeiro. Reuters

Bayan lallasa karamar kasar Tahiti ci 10-0 a gasar cin kofin zakarun Nahiyoyin Duniya a Brazil, a ranar Lahadi ne Spain za ta kara da Najeriya, kuma maki daya ne kacal 'Yan wasan Spain ke nema su tsallake zuwa zagayen dab da na karshe.

Talla

Fernando Torres da David Villa su ne ‘Yan wasan da suka yi wa Spain ruwan kwallaye a ragar Tahiti bayan Vicente del Bosque ya ajiye zaratan ‘Yan wasan shi irinsu Xavi da Iniesta da Fabregas domin kece raini da Najeriya.

Spain tana bukatar maki daya kafin ta tsallake zagayen dab da na karshe, kuma Najeriya sai ta lallasa Spain akalla ci 4 kafin Super Eagles su haramta wa Spain tsallakewa idan Uraguay ta lallasa Tahiti.

Kashin da Najeriya ta sha a hannun Uraguay shi ne ya dagula wa Stephen Keshi lissafi.

Idan har Uraguay ta doke Tahiti kamar yadda aka yi hasashe, ya zama dole zai Najeriya ta doke Spain kafin ‘Yan wasan Super Eagles su tsallake zagayen dab da na karshe. Amma Keshi yace bai cire rai ba.

“Komi na iya faruwa” a cewar Keshi.

A gasar cin kofin Duniya da aka gudanar a Faransa a shekarar 1998, Najeriya ta doke Spain ci 3-2.

Kashin da Najeriya ta sha a hannun Uruguay shi ne ya kawo karshen buga wasanni 18 ba tare da samun galabar Super Eagles ba, yayin da rabon Spain ta sha kashi a gasa tun lokacin da Switzerland ta samu sa’arta a farkon gasar cin kofin duniya a shekarar 2010 wanda Spain ta lashe a kasar Afrika ta Kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI