Wasan Tennis

Bude gasar Wimbledon a bana

Gasar Wimbledon
Gasar Wimbledon

A yau ne za a fara fafatawa a gasar Wimbledon inda a bangaren maza Roger Federer zai fara karawa da dan kasar Romania Victor Hanescu, a yayin da Andy Murray zai kara da Benjamin Becker dan kasar Jamus.

Talla

Shi kuwa Rafael Nadal wanda ya lashe gasar Rolland Garros a kwanan nan zai fafata ne da Steve Darcis dan kasar Belgium.

A bangaren mata kuwa, Maria Sharapova za ta fara karawa ne da Kristina Madenovic.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI