Italiya

Kotun Italiya za ta yanke hukunci kan tuhumar da ake wa Berlusconi

Tsohon Firaministan Italiya, Silvio Berlusconi
Tsohon Firaministan Italiya, Silvio Berlusconi REUTERS/Remo Casilli

Yau ake saran wata kotun kasar Italiya, za ta yanke hukunci kan tuhumar da akewa Tsohon Firaministan kasar, Silvio Berlusconi, na baiwa wata yarinya mai karancin shekaru kudi dan lalata da ita, laifin da aka ce ya sabawa rantsuwar ofishinsa.

Talla

Masu gabatar da kara, sun nemi haramtawa Berlusconi rike wani mukamin siyasa har abada, da kuma daurin shekaru shida a gidan yari.

Masu sharhi na ganin idan har aka sami Berlusconi da laifi, hakan zai iya kawo mai cikas ga muradansa na siyasa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI