Afrika ta Kudu

Rashin lafiyar Nelson Mandela ta yi tsanani

Tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, Nelson Mandela
Tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, Nelson Mandela REUTERS/Mike Hutchings

Rahotanni daga fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu, na cewa, rashin lafiyar tsohon shugaban kasa Nelson Mandela ta yi tsanani yayin da ya kwashe sama da makwanni biyu yana karbar magani a Asibiti. Wanna shi ne karo na farko da rashin lafiyar ta Mandela ta yi tsanani tun bayan kwantar da shi da aka yi a asibitin da ke birnin Pretoria.

Talla

“Rashin lafiyar tsohon shugaban kasa Nelson Mandela wanda har yanzu yana kwance a Asibiti ta yi tsanani.” Inji Kakakin fadar shugaban kasa, Mac Maharaj.

A lokacin da aka kwantar da shi a asibiti, rahotanni sun ce Mandela dan shekaru 94 yana cikin wani mawuyacin hali sai dai bai fita daga cikin hayyacin shi ba.

A ranar Lahadi ne shugaban kasar, Jacob Zuma ya ziyarci Mandela a asibiti, inda likitocin da ke kula da shi suka bayyana mai cewa lafiyar shi na tabarbarewa.

Wannan ne karo na hudu da Mandela  ke kwanciya a asibiti  tun daga watan Disambar bara saboda fama da ya ke yi da cutar huhu na wani tsawon lokaci.

Shugaba Zuma ya yi kira ga ‘yan kasar da ma daukacin mutanen duniya da su dukufa wajen yi wa Mandela addu’ar samun sauki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI