Amurka-Rasha

Snowden na shirin ficewa daga Rasha zuwa Ecuador

Edward Snowden, mutumin da Amurka ke nema ruwa a jallo
Edward Snowden, mutumin da Amurka ke nema ruwa a jallo © 2013 Praxis Films / Laura Poitras

Tsohon jami’in leken asiri na kasar Amurka, Edaward Snowden na shirin ficewa daga kasar Rasha zuwa Ecuador domin neman mafaka a dai dai lokacin da hukumomin Amurka ke nema Rashan ta mika mata tsohon jami’in.

Talla

A jiya lahadi Snowden, dan shekaru 30 ya isa birnin Moscow bayan ya fice daga Hong Kong a ci gaba da tserewa da ya ke yi daga hukumomin kasarsa.
Har ila yau a jiya, Amurkan ta janye paspo din Snowden a wani matakin dakile zirga zirgarsa, a yayin da shi kuma ya mika takardar neman izinin samun mafaka ga hukumomin Ecaudor.

Ecuador ta ce ta na nazari kan bukatar Edward Snowden ya mika mata a lokacin hada wannan rahoto.

Amurka na neman Snowden ruwa a jallo ne domin ya fuskanci tuhuma akan zarginsa da ta ke yi da satar bayanai tare da bayyanasu ga idon duniya, wanda hakan ya sa ta fitar da sammacin cafke shi a ranar Juma’a.

Snowden ya fallasa wani shiri ne da kasar ta Amurka ke yi na tatsar bayanan sirrin jama’a a sassa daban daban na duniya ba tare da sanin jama’a ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI