Pakistan-Amurka

Taliban ta dauki alhakin kashe ‘yan yawon bude ido 9 a Pakistan

Mayakan kungiyar Taliban
Mayakan kungiyar Taliban REUTERS

Kungiyar Taliban a kasar Pakistan, ta dauki alhakin kashe baki ‘Yan kasashen waje tara a Himalayas, dake yawon bude ido tare da dan rakiyarsu guda. Cikin wadanda ‘Yan bindigan suka kashe, akwai ‘Yan kasar China biyu, dan Amurka guda da dan Nepal guda, sai kuma wasu ‘Yan kasar Ukraine da Pakistan. 

Talla

An dai aikata kisan ne daren Asabar inda kungiyar ta yi ikrarin cewa za ta saka kai hare hare kan ‘yan kasar waje cikin manufofinta a matsayin rumukon hare hare da kasar Amurka ke kaiwa a Pakistan ta hanyar jirage marasa matuka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.