Kwallon kafa

Spain za ta kara da Italiya, Uruguay da Brazil a wasannin daf da na karshe

'Yan wasan Spain Fernando Torres da Raúl Albiol suna muranar lallasa 'Yan wasan Najeriya da ci 3-0
'Yan wasan Spain Fernando Torres da Raúl Albiol suna muranar lallasa 'Yan wasan Najeriya da ci 3-0 Reuters

Kasar Spain ta samu tsallakawa zuwa zagayen daf da na karshe, wato semi final a gasar cin kofin zakarun nahiyoyin duniya da ake bugawa a Brazil, bayan ta doke Najeriya da ci 3-0.

Talla

Za kuma ta kara ne da kasar Italiya a ranar Alhamis wacce suka lallasa da ci 4-0 a gasar cin kofin nahiyar Turai da aka buga a bara.

A yanzu haka rahotanni na nuna cewa dan wasan italiya Mario Balotelli ba zai samu damar buga wannan wasa ba saboda rauni da yak e fama da shi, kamar yadda hukumar kwallon kafar Italiya ta bayyana.

A daya bangaren cikin wasannin da aka buga, Uruguay ta tsallaka zuwa zagayen daf da na karshe bayan ta doke Tahiti da ci 8-0.

Yanzu Uruguay za ta kara ne da mai masaukin baki, Brazil a ranar Laraba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.