Gwamnatin Yobe a Najeriya ta rufe makarantu
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Jihar Yobe, ta bayar da umurnin rufe daukacin makarantun Sakandaren Jihar, sakamakon harin da aka kai a Mamudo, wanda ya hallaka dalibai 22 da malami guda. Gwamnan Jihar ne Ibrahim Geidam ya dauki matakin, yayin da ya kai ziyara a makarantar da aka kai hari. Ahmed Bedu Wakilin RFI a Yobe, ya aiko da rahoto.