Ra'ayin masu saurare game da taron kasashen Afrika a Abuja

Sauti 15:30
Taron shugaban kasashen Afrika da aka gudanar a Abuja a 2012
Taron shugaban kasashen Afrika da aka gudanar a Abuja a 2012 AFP PHOTO/Pius Utomi Ekpei

An bude taron shugabanin kasashen Afrika na musamman a Najeriya, inda shugabanin ke nazari game da ci gaban da ake samu wajen yaki da cutar kanjamau da cizon sauro da tarin fuka. Kuma cikin shugabanni 10 da suka halarci taron akwai shugaban Sudan Umar Hassan al Bashir wanda kotun duniya ke nema ruwa a jallo. Masu sauraren RFI Hausa sun bayyana ra’ayinsu game da taron shugabannin.