Italiya

Mutanen Masar da Syria sun tsallaka zuwa Italiya

REUTERS/Manuel Silvestri

Mahukuntan Italiya sun ce wasu jiragen ruwa guda hudu shake da ‘yan gudun hijira daga Masar da Syria sun isa kasar, wadanda suka kauracewa rikicin da ke faruwa a kasasashen. Akwai kuma wani jirgi da ya kwaso ‘Yan Najeriya da Ghana zuwa kasar ta Italiya.

Talla

Jirgin farko ya isa kasar Italiya ne a yankin Catania dauke da mutane kusan 100, cikinsu kuma kawai mata 17 da yara kanana 11. Kuma mahukuntan Italiya sun ce bakin hauren sun fito ne daga Syria da Masar domin tsira da rayuwarsu saboda rikicin da ake ci gaba da yi a kasashen.

Daya daga cikin bakin hauren ya shaidawa kamfanin Dillacin labaran kasar na Italiya cewa sun kwashe tsawon mako guda kafin iso.

Wani jami’in kasar Italiya yace akwai mutane shida daga cikin bakin hauren da aka kwasa zuwa Asibiti.

Wani jargin kuma ya kwaso mutane ne 150 zuwa kasar ta Italiya kuma bakin hauren sun fi to ne daga Syria.

Akwai kuma ‘Yan Najeriya da kasar Ghana guda 77 cikin bakin haure da suka tsallaka zuwa Italiya, domin an dade ana fataucin Mata zuwa kasar Italiya domin aikin karuwanci, wasunsu da dama ne aka koro zuwa Libya inda yawanci nan ne hanyar da ‘Yan Najeriya ke bi zuwa shiga kasar Italiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.