Najeriya

Shugaba Goodluck na Najeriya ya sallami Ministoci Tara.

shugaba Jonathan na Najeriya
shugaba Jonathan na Najeriya Reuters/Afolabi Sotunde

Ministocin da shugaba Goodluck Jonathan ya sallama dai sun hada da karamin Ministan tsaro Mrs Olushola Odana, da ta Makamashi Hajiya Zainab Kuchi, da na Ayyukan Gona Alhaji Bukar Tijjani.

Talla

Sauran sun hada da na kimiyya da fasahar kere-kere Mr Ita Okon Bassey, data Ilimi Parfesa Rukayyat Ahmad Rufa’I da kula da muhalli Hajiya Hadiza Ibrahim mai Lafiya da ta kula da Gidaje da tsara Birane Mrs Ama Peple da na kula da muhimman tsare-tsare Dr Shamsudden Usman da na kula da harkokin waje Mr olUBENGA Ashiru.

A halin da ake ciki kuma an umrci wasu Ministocin da aba’a kora ba, da su kuma da wasu daga cikin Ma’aikatun da aka kori Ministocin su.

Wannan kuwa har ya zwa lokacin da za’a nada wasu Ministocin.

Ministan watsa labarai Labaran Maku, zai kula da Ma’aikatar tsaro, karamin Ministan Ilimi kuma ya kula da ma’aikatar, sai Mrs Viola Owuliri ta kula da ma’akatar harkokin waje, a yayin da karamin Ministan ayyuka Ambasada Bashir Yuguda ya kula da da muhimman tsare-tsare na kasar.

Arc Musa Sada na Ma’adanai zai kula da ma’akatar Gidaje da tsara birane.

Ministan Makamashi Professor Chinedu Nebu zai kula da Ma’aikatar ma’akatar bayan ficewar ta Ilimi Rukayyat Ahmad Rufa’i.

Ma’akatun Niger Delta da Kimiyya da Fasahar Kere-kere zasu kasance ne karkashin kulawar Mrs Omobola Johnson ta ma’akatar sadarwa da kimiyyar kere-kere, ta aikin Gona kuwa, ta kasance a kulawar Dr Akinwumi Adeshina.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.