Alhaji Abubakar Cika, Tsohon Jekadan Najeriya a Iran

Sauti 02:55
Wakilan manyan kasashen Duniya suna tattaunawa da Iran a Geneva
Wakilan manyan kasashen Duniya suna tattaunawa da Iran a Geneva REUTERS/Jean-Christophe Bott

An watse zaman tattaunawa tsakanin kasashen Duniya da Iran a karshen mako ba tare da bangarorin biyu sun samu fahimtar juna ba akan batun Nukiliya da suke son Iran ta dakatar da shirinta, amma  Hukumar makamashin Nukiliya ta duniya IAEA, ta ce ta cim ma jituwa tsakaninta da Mahukuntan Iran a kan jadawalin da bangarorin biyu za su yi tattaunawa akai nan gaba. Shin ko taron zai yi tasiri a karshe? Mahmud Lalo ya tattauna da Alhaji Abubakar Cika, Tsohon jakadan Najeriya a Iran