Najeriya

‘Yan wasan Golden Eaglets sun kwashi kudi a Najeriya

Matasan Najeriya suna murnar lashe kofin gasar cin kofin 'Yan kasa da shekaru 17 a filin wasa na Mohammed Bin Zayed a Abu Dhabi
Matasan Najeriya suna murnar lashe kofin gasar cin kofin 'Yan kasa da shekaru 17 a filin wasa na Mohammed Bin Zayed a Abu Dhabi REUTERS/Ahmed Jadallah

Bayan da ‘Yan wasan Golden Eaglets na Najeriya suka lashe wa Najeriya kofin Duniya na ‘Yan kasa da shekaru 17, Shugaban Tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan ya dankarawa ‘Yan wasan kudi, kowannensu Naira Miliyan biyu saboda nasarar da suka samu na lashe kofin gasar bayan sun caccasa matasan Mexico ci 3-0 a wasan karshe da aka gudanar a Abu Dhabi.

Talla

Jonathan ya ba Mai horar da ‘Yan wasan, Manu Garba Miliyan uku, mataimakinsa kuma kudi Naira Miliyan Biyu da rabi.

A lokacin da ya ke jawabi shugaba Jonathan yace wannan nasara ce ga mutanen Afrika baki daya kuma wani tafarki ne na farfado da wasan kwallon kafa a Najeriya.

Dan wasan Najeriya ne Kelechi FIFA ta zaba gwarzon dan wasa, wanda ya jefa kwallaye 6 a raga.

Yanzu haka kuma akwai kungiyoyin Turai da suke neman sayen dan wasan, kuma Rahotanni sun ce Arsenal tana cikin kungiyoyin da ke sahun gaba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.