Bakonmu a Yau

Dr. Imran Abdulrahman, Malami a Jami’ar Jos a Najeriya

Sauti 03:27
ginin Ofishin hukumar kare hakkin Bil'adama ta Human Rights Watch, à Moscow
ginin Ofishin hukumar kare hakkin Bil'adama ta Human Rights Watch, à Moscow REUTERS/Maxim Shemetov

A daidai lokacin da kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ke fitar da wani rahoto kan tashe tashen hankula, da suka ki ci suka ki cinyewa a yankin tsakiyar Najeriya, kafafen yada labarai sun sami wani bangaren rahoton da ke cewa matsalar na faruwa ne sakamakon nuna halin ko in kula daga bangaren hukukomi. Nasiruddeen Muhammad ya tattauna wannan batun, da Dr Imran Abdulrahman, malami a Jami’ar Jos, kuma jami’in da ke kula da Jihohin Flato da Kaduna, a cibiyar samar da zaman lafiya ta Nigerian Stability and reconciliation Programme, da ke karkashin gwamnatin Britaniya.