Najeriya

‘Yan sanda sun dakile yunkurin kai wani sabon hari a Kano

Inda aka kai hari a Jihar Kano dake tarayyar Najeriya
Inda aka kai hari a Jihar Kano dake tarayyar Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde

‘Yan sanda a Jihar Kanon Najeriya sun sanar da kawar da wani yunkurin kai wani sabon harin da aka shirya kaiwa, bayan da harin da aka kai a yankin Sabon Gari ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyar. Wasu rahotanni sun ce mutane hudu ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata.

Talla

‘Yan sandan sun kaucewa yunkurin ne wanda aka shirya kai shi a cikin wata mota da suka tsayar wacce ke dauke da kayyakin hada bama bamai.

“Mun kaucewa aukuwar wani harin ne bayan da muka samu bayanan sirri da suka nuna cewa wata mota kirar Mitsubishi ba dauke da wadannan kayayyaki na hada bom.” Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan Jihar ta fitar ta bayyana.

A cewar sanarwar, a kan titin Tafawa Balewa dake yankin Nasarawa a Kano aka samu motar.

Harin na baya bayan nan ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyar ne a wani wajen shakatawa inda mutane biyar suka rasa rayukansu ciki har da wata yarinya ‘yar shekaru 12, a cewar Shugaban rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, Adelere Shiniba.

A ranar Asabar din da ta gabata aka gudanar da zaben kananan hukumomi, inda jam’iayr adawa ta kada jam’iya mai mulki ta Shugaba Goodluck Jonathan.

Yanzu haka hukumomi sun ya yi wuri a fara nuna yatsa ga wanda ked a alhakin kai wannan hari a yankin na Sabon Gari wanda mafi yawan mazauna yankin mabiya addinin kirista ne.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI