Najeriya

Mutane 6 ne suka rasu sanadiyyar tashin bam a Jos Najeriya

Tagwayen hare haren bama bamai da aka kai a garin Jos a Najeriya, ranar Talata
Tagwayen hare haren bama bamai da aka kai a garin Jos a Najeriya, ranar Talata AFP

Mutane 6 sun mutu da dama suka sami raunuka, lokacin da wani dan kunar bakin wake yayi yunkurin tada bam, a wani wajen kallon kwallo, da ke garin Jos, a arewacin Nigeria. Wani mazaunin birnin mai suna Haruna Muhammad, daya garzaya inda lamatrin ya faru ya shaida wa gidan Radiyon Faransa cewa, mutanen sun sami raunuka ne, a lakacin da suke yi yunkuri tserewa daga wajen kallon, da ke kusa da inda lamarin ya faru.Ko a ranar Talata da ta gabata saida wasu bama baman suka tashi a wata kasuwar da ke tsakiyar birnin, Lamarin daya yi sanadiyyar mutuwa kusan mutane 200.A cikin watannin da suka gabata an sami kwara kwaran zaman lafiya a birnin na Jos, sai dai masu lura da lamura na ganin tashe tashen bama baman zasu iya dawo da hannun agogo baya.