Najeriya

Mutane da dama sun mutu a hare haren Boko Haram a kauyuka 3

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau
Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau Capture d'écran d'une vidéo de Boko Haram - AFP

Jerin hare haren da ‘yan bindiga suka kai wasu kauyuka 4, a yankin arewa maso gabashin Nigeria mai fama da tashe tashhen hankula, sun yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Mazauna kauyukan sun tabbatar da aukuwar hare haren da suka afku jiya Asabar a kauyukan Nuwari, Musari, da Walori, da ke yankin Gamboru Ngala a kusa da kan iyaka da Kamaru.Wadannan sune na baya bayan nan a jerin hare haren da ake danganta su da ‘yan kungiyar nan ta Boko Haram a yankin.Sai dai har yanzu rundunar sojan kasar bata tabbatar da hare haren na Jihar Borno ba, da ta fi fama da tashe atshen hankulan ‘yan bindigar da aka shafe shekaru 5.