Nigeria

Sojojin Najeriya sun yi wa wata jarida dirar mikiya

Babban hafsan Sojin Najeriya Laftanal Janar Kenneth Minimah
Babban hafsan Sojin Najeriya Laftanal Janar Kenneth Minimah REUTERS/Joe Penney

Sojojin Nigeria sun hana rarraba jaridar Daily Trust da ake bugawa a birnin Abuja, bayan da a kwanakin baya jaridar ta dauko wani labarin da kezargin wasu janarorin sojan kasar da almundahana. Hukumomin kamfanin jaridar sun ce sojoji dauke da muggan makamai sun dakatar da rarraba jaridar daga cibiyoyin da ake bugata a Abuja, Kano da Borno, inda suka yi bude shafukanata don neman abinda suka kira, labarum da ka iya tayar da zaune tsaye.Sai dai mai Magana da yawun sojan ya shaida wa kamfanin dillancin labarun Faransa cewa sun gudanar da bincike ne kawai a cikin motocin rarraba jaridun, sannan a barsu su wuce.Sojojin Nigeria na ci gaba da fuskantar matsin lamba, sakamakon kasa kawo karshen rikincin Boko Haram, daya lakume rayukan dubun dubatar ‘yan kasar.