Najeriya

An tabbatar da zaben sabon Sarkin Kano malam Sanusi Lamido Sanusi

Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi
Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi RFI Hausa

A Najeriya Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da mika sarautar Kano ga sabon Sarkin da aka zaba bayan rasuwar marigayi Mai martaba Alhaji Dr. Ado Bayero a karshen Mako.To ko wanene sabon Sarkin Kanon, ga dai dan takaitaccen Tarihinsa. 

Talla

TARIHIN SABON SARKIN KANO

Tarihi dai ya nuna cewar a shekaarra 1961 ne aka haifi sabon Sarkin Kano Malam Sanusi Lamido Sanusi a ranar 31 ga watan Yuli.

Wannan dai ya nuna cewar sabon sarkin na da shekaru 2 ne kacal aka nada wanda ya gada wato marigayi Dr Ado Bayero a shekarar 1963.

A bangaren karatu kuwa sabon Sarki Malam Sanusi Lamido sanusi ya yi Digirin farko ne a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya a fanning tsimi da tanadi, sai kuma wani digirin a jami’ar Khartoum ta kasar Sudan.

Sabon Sarkin ya dan yi koyarwa kadan a Jami’ar Ahmadu Bello kamin daga bisani ya koma aikin Banki a 1985 a Icon Limited da kuma Bankunan UBA da First Bank.

A nan ne fa Sanusi Lamido Sanusi ya kara samun ci gaba zuwa Gwamnan babban Bankin Najeriya a 2009.

Shi ne ya bankado badakalar wwaure kudi a baitul malin Najeriya abinda ya haifar da matsala tsakaninsa da hukumomin kasra ta Najeriya suka kuma saukar da shi daga kan jagorancin babban Bankin kasar a ran 20 ga Fabrarirun 2014, yanzu kuma shi ne sabon Sarkin Kano.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI