Najeriya

‘Yan Jarida a Najeriya sun kalubalanci gwamnati kan hana sayar da Jaridu

news papers

A Najeriya ana ci gaba da yin tsokaci kan zargin hana sayar da wasu jaridu da sojin a tarayyar Najeriya ke yi. Ko a karshen makon da ya gabata ma Dakarun Najeriya sun hana Kamfunnan Jaridu kamar Daily Trust da Punch sayar da Jaridunsu

Talla

Wannan dai ya biyo ne bayan da jaridun suka buga wani labari dake nuna yadda matsalar rashawa ta yi katutu a bangaren sojin kasar.

Jaridun da suka hada da Daily Trust da ake bugawa a yankin Arewacin kasar, da ta The Nation da Leadership da kuma Punch dukkaninsu sn yi Allah wadai da matakan da Sojin kasar suka dauka na hanasu aikinsu.
Shugaban Kungiyar ‘yan jarida ta kasa a Najeriya Muhammad Garba ya ce abin ya basu mamaki domin a tunanin duk wani dan Najeriya mulkin Dimokradiyya ake yi.

Kuma a cewarsa, za su yi taron gaggawa domin tattauna yanda za su fuskanci wannan matsalar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.