Bakonmu a Yau

Umar Faruk Musa

Sauti 03:09
Wani dandalin sayar da jaridu
Wani dandalin sayar da jaridu AFP / HABIBOU KOUYATE

Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama ta SERAP a Najeriya, ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta janyo hankalin gwamnatin Najeriya kan abinda ta kira karan tsaye da take yiwa kafofin yada labaran kasar, wanda ya kaiga hana raba wasu jaridu a cikin kasar da kuma tsare wasu ma’aikatan kafofin yada labaran. Umar Faruk Musa, shugaban tashar Vision FM da ke Abuja da aka hana gudanar da wani shiri da ake kira Idon Mikiya ya yi mana tsokaci kan wannan lamari kamar yadda za ku ji a tattaunawar su da wakilinmu Kabir Yusuf.