Najeriya

Al’ummar Fulani a Najeriya sun damu da sace Matansu 40 da aka yi

theinfrastructurenewsn...

A Najeriya yanzu haka rahotani dake karo da juna na bayyana cewa al’umar Fulani kasar na iyakacin kokarin gani an ceto matan nan da wasu yan bidinga da ake zato yan kungiyar boko haram ne suka sace, kamar dai yanda Shugaban Fulani Kungiyar Miyeti Allah ta kasa Alhaji Kirowa Ardo Zuru yake mai cewa

Talla

Yace dukkann alummar Fulani sun damu da wannan kamun da aka yiwa Matan Fulani.

Alhaji Kirowa Ardo Zuru ya kara da yin kira ga Gwamnatin tarayyar akan bayanin da ta yi na kokarin kwato Matan, da ta kara kaimi domin matsalar ta shafi al’umma ne ba mutum Daya ba.

Bisa haka Kiruwa ya bukaci al’ummar Najeriya da su komawa Allah don abinda ya kira musibar da ta sauka a kasar sakamakon hare-haren ‘ya’yan kungiyar Boko Haram.

Kame Matan Fulanin dai ya biyo ne bayan irinsa da ya auku na kame ‘yan Matan Chibok da Kungiyar Boko Haram ta fito fili ta bayyana daukar alhaki.

Sai dai bayan kwashe akalla Watanni 2 wadannan yan Matan na hannun ‘ya’yan kungiyar Boko Haram ba tare da an ya kwatosu ba, masu lura da al’amurra na ganin cewar Gwamnatin Najeriya dai ta kasa duk da gayyato kwararru da ta yi daga kassahen Amurka da Faransa da Burtaniya da kuma Israela.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.