Najeriya

An shiga rana ta 63 da sace ‘yanmatan Chibok a Najeriya

omoooduarere.blogspot.com

Majalisar Dunkin Duniya ta ce rashin tsaro na barazana ga yunkurin ilmantar da ‘ya’ya mata a Nigeria, yayin da aka shiga rana ta 63 da sace dalibai mata sama da 200 a yankin Arewa maso gabashin Najeriya ba tare da gano inda suke ba

Talla

Sanarwar da hukumar kula da yara, ilimi, kimiya da al’adu ta Majalisar Dunkin Duniya ta bayar kan bikin ranar Dan Afrika da akeyi yau Litinin, ya ce iyaye na jan kafa wajen sanya ‘ya’yan su a makaranta a Yankin Arewa maso Gabashin Nigeria.

Sanarwar ta ce yanzu haka yara miliyan 10 da rabi ne ba sa zuwa makaranta a Nigeria, wanda adadin shi ne mafi girma a Duniya.

Sanarwar ta kuma ce kashi 60 na wadanan yara ‘ya’ya mata ne, kuma suna Arewacin Nigeria ne.

Rahotan kungiyar ya kuma ce kowanne daya cikin uku na yaran da ya kamata a ce suna a makarantun furamare ne kuma basa zuwa makaranta, yayin da kowanne daya cikin 4 na masu zuwa kananan makarantun Sakandare sun daina zuwa makarantar.

Rahotan ya kuma kara da cewar, matsalar tsaron da ake fuskanta a Arewacin kasar ta tilastawa yara daina karatu, domin rufe makarantun da akayi, duk da bukatar iyayen su na ganin sun samu ilimi, da kuma tallafin da kasar Burtaniya ke bayar wa wajen ganin an ilmintar da yara mata miliyan daya kafin shekarar 2020.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.