Najeriya

Koken iyayen dalibai na Chibok zuwa Gwamnatin Najeriya

Wasu daga cikin 'Iyayen Matan da aka sace 'yayansu a Chibok Jihar Borno a Najeriya.
Wasu daga cikin 'Iyayen Matan da aka sace 'yayansu a Chibok Jihar Borno a Najeriya. DR

A Nigeria, iyayen dalibai mata 200 da aka sace daga makarantar mata dake garin Chibok a jihar Borno sun nemi hukumomin kasar dasu fito fili su bayyana masu gaskiyar halin da ake ciki ganin yadda aka kwashe watanni biyu babu bayani.Yanzu haka dai iyayen ‘yan matan kusan kullun a gidan shugaban makarantar Hajiya Asabe suke wuni har lokacin da zasu samun bayanai gameda ‘ya’yan su.  

Talla

A dai wajen Rundunar Sojan Najeriya tace tana nazarin bin dubarun da kasar Sri Lanka ta bi ta karya mayakan Tamil Tigers, domin share al’amarin ‘Yan kungiyar Boko Haram a kasar, bayan wata tawagar manyan Jami’an Sojin Sri Lanka sun kawo ziyara a Najeriya.
An shafe Shekaru ana yakin basasa a Kasar Sri Lanka kuma sai a 2009 ne kasar ta kawo karshen mayakan Tamil Tigers.

Amma Fasalin Sri Lanka na yakar ‘yan tawayen ya sha suka daga kasashen duniya saboda irin hasarar rayukan fararen hula da aka samu a tsawon shekaru 30 da suka fafata.
Wannan kuma na zuwa ne bayan Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya gana da takwaransa na Pakistan Mamnoon Hussain akan yadda za su hada hannu domin yaki da ta’addanci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.