Najeriya

Sojojin Najeriya na cigaba da kama mutane a kasar

Sojoji a jihar Abia da ke kudu-maso gabaci  Najeriya sun sanar da kama  wasu 'yan arewacin kasar kimanin 500 bisa zargin cewa 'yan kungiyar  Boko Haram ne.

Talla

Rahotanni daga yankin na nuni da cewa mutanen da suka futo daga jihar Jigawa , masu zuwa birnin Fatakwal na jihar Rivers domin gudanar da harkokin kasuwanci da kuma ci-rani..

A dai bangaren kuma jami’an tsaro a Jihar Filato sun sanar da samu nasarar ceto wani dan kasar Birtaniya da aka sace a jihar dan neman diyya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.