Najeriya

Bom ya tashi a garin Bauchi dake Nigeria

Wani jami'in tsaro na gadin inda aka kai harin Bom a Nigeria
Wani jami'in tsaro na gadin inda aka kai harin Bom a Nigeria REUTERS/Afolabi Sotunde

Rundunar ‘Yan sandan Nigeria a jihar Bauchi, tace Bom ya tashi a wani Otel mai suna Peoples Hotel, dake yankin bayan gari, a birnin na Bauchi.Mai maganar da yawun rundunar ‘Yan Sandan jihar DSP Haruna Mohammed, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace mutane 10 sun mutu, yayinda wasu 14 suka sami raunuka sakamakon fashewar.Wakilinmu a jihar ta Bauchi Shehu Saulawa ya ce jami’an tsaro sun killace yankin da lamarin ya faru, inda suke ci gaba da gudanar da bincike.