Najeriya

An fara azumin watan Ramadan a Najeriya

Mai alfarma sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar
Mai alfarma sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar

Yau Asabar al’ummar Musulmin Nigeria suka fara Azumin watan Ramadan na wannan shekarar. Fadar mai martaba sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar ce ta bada sanarwar ganin sabon watan na Ramadan.
Wakilinmu na Sokoto Hassan Sahabi Sanyinnawal wanda ya kwashe dare a fadar sarkin musulmin, yace Shugaban kwamimitin kula da ganin wata na majalisar Sarkin Musulmi Professor Sambo Wali Junaidu, wanda ya bada sanarwar yace an samu sanarwar ganin sabon watan Ramadan daga sarakunan Gwandu da Argungu dake jahar Kebbi da kuma Isa da Durbawa a jahar Sokoto.