Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Azumin watan Ramadana

Sauti 15:30
Musulmi suna ibada a watan Azumi
Musulmi suna ibada a watan Azumi RFI/Sun Mesa

Al’ummar Musulmi a daukacin Duniya na ci gaba da gudannar da Azumin Ramadana, da suke yi a kowace shekara domin samun tsananin kusanci da Allah Madaukakin sarki. Malami dai sun bayyana cewar Azumi na a matsayin garkuwa ne ga al’ummar Musulmi daga shiga Wuta. Akwai kuma sharudda da ka’idojin da Musulunci ya shata akan Musulmi masu Azumi. Yau akan wannan shirin zai tattauna tare da Abdoulaye Issa.