Isa ga babban shafi
Najeriya

Rundunar Sojin Najeriya ta gurfanar da Sojinta kan bore a Bariki

Zubin rubutu: Faruk Yabo | Garba Aliyu
2 min

Rundunar tsaro ta Nigeria ta gaskata cewa ta gurfanar da wasu sojojinta a gaba kotun ta da ke hukunta masu laifi, saboda hannu da suke da shi wajen yin bore a wani barikinsu da ke Maiduguri jihar Borno da ke fama da rikicin ‘yan Boko Haram

Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wani bincike na Hukumar tsaron kasar Africa ta kudu ke cewa lamarin yakar Boko Haram yafi karfin Dakarun Nigeria.

Kakakin rundunar Tsaro ta Nigeria Major Janar. Chris Olukolade ne ya bayyana cewa akwai wadanda aka gurfanar da su a gaban kotun saboda a hukunta su.

A watan da ya gabata ne dai aka sami labarin da ke nuna wasu kananan soji da ke Bama a Jihar Borno sun fusata da wani kwamandansu saboda zargin yana kwanciya kan hakkin su, da kuma kin kulawa da rayukansu sosai.

A chan baya dai wasu kananan sojin kasar da ke chan suna fafatawa da ‘yan Boko Haram kan kira wayoyin kafunnan kafafen yada labarai na kasashen waje da bayanai marasa dadin ji na yadda wasu kwamandojinsu, ke wasu take-take da ke nuna muraran suna da masaniyar ayyukan ‘yan kungiyar Boko Haram.

Su kansu talakawa mazauna kauyuka da mukan tuntuba kan rika zargin wasu jamian tsaron da kin yin komi idan har sun tuntubesu cikin gaggawa suna neman dauki.

Yadda ma kawai yau aka kwashe watanni uku da sace ‘yan matan makarantar Sakandaren Chibok a Borno kawai, Sojin kasar na cewa sun san inda yaran suke amma an kasa ceto su yasa wasu ‘yan Nigeria yiwa sojan kasar kallon hadarin kaji.

Hajiya Asabe itace shugaban makarantar ‘yan matan da ke a Chibok kuma tace soja na kokarinsu amma ya kamata su taimaka game da batun dalibanta.

Wannan kuwa a cewarta saboda yanda Iyayen Yaran kan wuni suna zuwa Makarantar don neman bayani kan halin da ake ciki a batun ceto ‘ya’yan nasu.

Mun yi iyakacin kokarin tuntuban Major Janar Chris Olukolade domin neman Karin bayani game da matakan da suke dauka don hukunta sojojin nasu amma kuma bai dauki wayar ba, amma kuma kamar yadda wannan bawan Allah ke cewa biri yayi kama da mutun.

A waje daya kuma Majiyoyin sirri na kasar Africa ta kudu na nuna cewa lamarin yakar ‘yan kungiyar Boko Haran ya fi karfi sojan Nigeria.

Jamian kasar Africa ta kudun na gugar zana ne a gaban Ministan tsaro na kasar China wato Sin, da ya ziyarcesu, sun kuma janyo hankalin China ga sauran matsalolin da suka dabaibaye Nigeria kamar batun ‘yan tsageran Niger Delta.

Cibiyar Tsaro ta kasar Africa ta kudu dai itace ke tattarowa kasar tasu bayanai na sirri gameda tsaro a kasashen duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.