Najeriya

Rikici na ci gaba da zafafa tsakanin 'yan majalisar jihar Nasarawa da babban Alkalin Jihar

Gwamnan jihar Nasarawa Umaru Al-makura na rantsuwa
Gwamnan jihar Nasarawa Umaru Al-makura na rantsuwa

Da alama takun saka na ci gaba da zafafa tsakanin majalisar dokokin jihar Nasarawa a arewacin Nigeria, da babban alkalin jihar Umaru Dikko, kan irin mutanen da ke cikin kwamitin da ke binciken gwamnan jihar Umaru Al-Makura. ‘Yan majalisar sun ce sun soke kwamitin da babban alkalin ya kafa, da suke so ya duba laifukan da suke zargin Gwamnan don zige shi.Dama la’ummar jihar sun nuna adawa da yunkurin tsige gwamnan nasu, inda suka yi zanga zangar data sa bangaren ‘yan majalisar, dake neman tsige gwamnan suka koma zamansu a wajen Lafiya, babbana birnin Jihar.