Boko Haram

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya ce yana nan da ransa.

Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau
Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau AFP

Shugaban kungiyar Boko Haram a tarayyar Najeriya Abubakar Shekau ya fidda sabon Bidiyo inda yake karyata rahoton da Rundunar Sojin Najeriyar ta bayar cewar ta kashe shi a wani gumurzu da ya gudana a baya

Talla

A wani sakon Bidiyon da Kamfanin dillancin labarai na AFP ya sama daga kungiyar, Abubakar ya bayyana cewar yana nan a raye kuma ma suna aiwatar da shara'a irin tasu a karkashin Daular da suka kafa. Abubakar Shekau ya fada a sabon Bidiyon cewar ba zai mutu ba, sai Allah ya karbi rayuwarsa.

 

Sabon Hoton bidiyon na mintoci 36 ya nuna Abubaka Shekau sanye da wasu Kubuttan Takalmin Rob abakake, yana tsaye a bayan wata Tankar Yaki da ke harba harssahe mai kakkabo Jirage ta sama.

 

Idan ana iya tunawa dai a Makon jiya ne Dakarun Najeriya suka fitar da Rahoton cewar sun kashe wani mutum mai ikrrain cewar shi ne Shekau a wata arangama da suka yi da 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram a wani yanki na Arewa maso gabashin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.