Najeriya

Janyewar Gwamnan Kwara daga takarar Shugabancin Najeriya

Gwamanan Kwara State ,Saraki Bukola
Gwamanan Kwara State ,Saraki Bukola

Tsohon Gwamnan Kwara Sanata Bukola Saraki ya sanar da janye takarar neman shugabancin Najeriya a karkashin jam'iyyar APC saboda abinda ya kira bukatar hada kai dan ceto kasar.Saraki ya sanar cewar kowa ya san dalilan da shi da wasu fitattun mutane suka bayar na barin PDP mai mulki dan komawa APC saboda haka ba zasu bari rarrabuwar kawuna ya shiga tsakanin su ba a lokacin da suke neman kawo sauyi.

Talla

Sanatan yace dan takara daya jam'iyar zata zaba a zaben fidda gwani saboda haka ya dace su hada kai maimakon bude kofar rikicin da kan iya zuwa bayan zaben cikin gida. Saraki yace yanzu lokaci ne na sadaukar da rai ba neman biyan bukata ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.